Gwamnatin jihar Katsina ta kaddamar da aikin bud’e samar da Tsaftattacen Ruwan sha wanda ya lashe Naira Milyan Dubu ukku da Tamanin 3.080,000,000 a cikin unguwanni takwas dake birnin Katsina.
A Ranar Alhamis 29/5/2025, Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda Phd CON ya kaddamar da aikin samar da Ruwan a rukunin gidaje na Asibiti Gwamnatin Tarayya dake cikin birnin Katsina.
Aikin samar da Ruwan Shan, anyi shi a cikin unguwanni takwas dake cikin birnin Katsina, inda aka samar da rijiyoyi burtsatse na zamani wanda zasu samar da Ruwan.
Unguwanni da aka gudanar da aikin sun had’a da sabuwar Unguwa, Rahama/ Abbatoir, Makera, Bayan NYSC, Dutsen-Safe, Rukunin gidaje na Barhim, Rukunin gidaje na Asibiti Gwamnatin Tarayya.
Da yake gabatar da jawabin shi Malam Dikko Radda Phd CON ya bayyana cewa” Garin Katsina yana fama da matsalar ruwan sha,Tun tsarin da akai na samar da Ruwan daga Ajiwa, Sama da shekaru hamsin da suka gabata, ba’a Kara aikin fadada aikin samar da Ruwan sha ba da wurin aje ruwa a cikin birnin Katsina sai wannan lokaci.
Ganin yadda al’umma suke ta Kara yawa suke shigowa a cikin birnin Katsina, ya sanya Gwamnatin jihar Katsina, ta ware Naira Milyan dubu ukku da Tamanin domin aikin samar da Ruwan a cikin birnin Katsina.
Ka zalika Gwamnatin jihar Katsina, ta sake ware Sama da Naira Milyan Dubu Ashirin da biyar domin sake bada aikin samar da Ruwan sha a cikin Garin Katsina da wasu Kananan Hukumomi a jihar Katsina.
Gwamna Radda yaci gaba da cewa” A kasafin kudin Bana Gwamnatin jihar Katsina, ta Kara ware Naira Milyan dubu Hamsin domin sake aikin samar da Ruwan sha kashi na biyu, daga Madatsar ruwa ta zobe, Dutsanma, Kankia, Charanchi, Kurfi,zuwa wasu garuruwa dake bisa hanya har zuwa Garin Katsina.
Mutane da dama suka tofa albarkacin bakin su daga ciki akwai kwamishinan ma’aitakar Ruwa Hon. Bishir Gambo Saulawa, Janaral Manaja na hukumar samar da Ruwan sha Engr, Dr Tukur Tingilin, Shugaban karamar Hukumar Katsina Hon. Isa Miqdad
Bikin wanda ya gudana a Rukunin gidaje na Asibiti Gwamnatin Tarayya ya samu halartar kakakin majalisar dokokin jihar Katsina, wanda ya samu wakilcin shugaban Masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Katsina Hon. Shamsu Abubakar Dabai, Shugaban hukumar cigaban Afrika Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri.
Sauran sun had’a da wasu daga cikin Yan majalisar zartarwa dana majalisar dokokin, shugaban karamar hukumar Katsina Hon. Isah Miqdad AD Saude Yan siyasa Maza da Mata da sauran su.