Domin Magance Matsalar Ruwa A Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Shugaban Hukumar Samar Da Ruwan Sha Ta jihar Katsina Injiniya Tukur Hassan Tinglin PhD, Ya Kai Ziyarar Gani Da Ido A Jamia’ar

Bayan labarai da suka riƙa yawo a kafafen sada zumunta na zamani, akan matsalar rashin ruwa da wutar lantarki a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, shugaban hukumar samar da ruwan sha ta jihar Katsina Injiniya Tukur Hassan Tingilin, ya ziyarci makarantar a yau Lahadi 25/05/2025, domin duba yadda za’a magance matsalar.

Da yake gabatar ma ɗaliban da jawabin shi Injiniya Tukur Tingilin, ya bayyana masu matsalar ta samu ne sakamakon ƙarancin lantarki da ake fama da ita a jihar nan, ya kuma tabbatar masu da za’ayi mai yiwuwa domin kawo ƙarshen matsalar.

“Kafin kawo ƙarshen wannan matsala, zamu tabbatar kowace rana tankunan motoci sun riƙa ɗauko ruwa suna kawo maku yadda zai wadata, kuma zamu samar da famfunan masu amfani da hasken rana domin kauce ma irin wannan matsalar anan gaba”

Daga cikin waɗan da suka tofa albarkacin bakin su a wurin akwai shugaban Makarantar Farfesa Shehi Salisu Mahammad, sai Kwamishinan ma’aikatar Ilimi mai zurfi Hon. Isah Muhammad Musa.